ZA A KAFA CIBIYAR \’YAN SANDAN MOPOL A KUDANCIN KADUNA

0
940

Daga Usman Nasidi

HUKUMAR ‘yan Sandan Najeriya za ta bude cibiyar MOPOL a Garin Kafanchan da ke Kudancin Jihar Kaduna. Wannan yana cikin kokarin Gwamnati na kawo karshen rikicin da ake ta yi tsakanin Fulani makiyaya da kuma mazauna gari.
Sufeta Janar na ‘yan Sanda, Ibrahim K. Idris ya bayyana haka a wani zama da ya yi da ‘yan jarida bayan da ya ziyarci inda rikicin ya faru a Kudancin Kaduhna. Sufetan ya ce ya zo da kan sa domin ya ga abin da ke faruwa.
Ya kara da cewa  ya tattauna da Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i inda ya bayyana cewa Hukumar ‘yan sandan kasar za ta bude cibiyar ‘yan sandan MOPOL a garin Kafanchan da ke Kudancin Kaduna.
Dama can Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana cewa za ta hukunta wadanda aka samu da laifin hura rikicin Yankin Kudancin Jihar Kaduna sannan a dauki mataki. Tun ba yau ba, an saba rikici a Yankin Kudancin Kadunan har ta kai gwamnatin tarayya za ta kafa Gidajen Soji har biyu a Yankin.
Mai Girma Gwamnan Jihar ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta kafa gidan soji a yankin domin kawo karshen wannan rikici. Gwamnan ya sanar da cewa gwamnatin tarayya za ta kafa gidajen soji har biyu a yankin a wata hira da ya yi kwanan nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here