Ya Yi Kira Ga Gwamnati Ta Tallafa Wa Kananan \”yan Kasuwa

0
877

Musa Muhammad Kutama, Daga Kalaba

MATSIN tattalin arzikin kasa ya sanya wani dan kasuw a mai suna Muhammad Anas Abubakar ya shawarci gwamnati da ta fito da wani shiri da zai rika tallafa wa kananan ‘yan kasuwa yadda suma za su bunkasa harkokin su musamman idan aka yi la’akari da yadda harkokin kasuwanci a kasar nan yake neman ya gagari mai karamin jari.

Dan kasuwar ya zanta da wakilinmu na kudanci a Kalaba Jihar Kuros Riba yayin da ya halarci kasuwar baje koli da ake yi

Ya ce “kamata ya yi gwamnati ta fito da wani shirin taimaka wa kananan ‘yan kasuwa ta hanyar samar masu da rancen kudi wandkowace shekara ta manya da kananan ‘yan kasuwa a Kalaba.a babu ruwa a cikinsa don su bunkasa sana’arsu, idan aka ce an bayar da rance da ruwa tamkar an yi wa mutum alheri ne da hannun dama a dawo a karbe da na hagu”.inji shi.

Muhammad Abubakar ya ci gaba da cewa kokawa da halin matsin tattalin arziki da ‘yan Najeirya ke kokawa ya shafi harkokinsa na saye da sayarwa tun da wasu lokutama kasar waje suke fita su sawo kayan kasuwar su farashin kudin kasashen waje ya yi tashin gauron zabi wanda hakan ya sanya kananan ,yan kasuwa suke ji a jikin su domin shi ma ya shafi sana’arsa “don babu wanda zai ce ba ta shafeshi ba saboda idan ka kula kayan na yawancin su shigowa ake yi da su daga waje, ka ga saboda yanayin yadda darajar takardar kudi naira ta fadi  a kasuwar musayar kudi  ya shafe mu matuka, misali ka ga abin da muke saya dubu 5. Yanzu sai ka saye shi  dubu 7 ko 8. Wanda a da kai za ka iya sayowa ma kasa da haka to ka ga ya fa ta irin wannan sannan kuma za ka zo nan ka yi ta fama da masu saye su ce ya yi tsada da sauran su “inji Abubakar

Har wa yau,dan kasuwar ya ce babban kalubalen da kasuwancinsa yake fama da shi shi ne, ba zai wuce harkar tsadar kayayyaki ba da ta tafiye-tafiye da muke yi gida da waje wajen sawo kaya da tafiya sayar da su ka ga kudin jirgi ya karu,kudin mota ma ya karu”.

Karshe dan kasuwa Muhammad Anas Abubakar ya kawo shawarar idan har gwamnati na son ta saukaka masu ,yan kasuwa  “shugaban kasa na iyakacin bakin kokarinsa na yaga ya saukaka w a’yan Najeriya halin da suke ciki babbar shawara ita ce ya kamata mu ‘yan najeriya mu koyi yin abubuwa da kan mu kuma mu koyi son namu na cikin gida da nuna kishin sa”.Ya yi fata yadda gwamanti ta yunkuro wajen kawo karshen halin matsi da ake kokawa da shi za ta fito wa da  kananan ‘yan kasuwa su ma  tasu mafitar  da za ta sanya su ma su ji sauki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here