An Kama Tsoho Dan Shekara 61 Da Yin Lalata Da Yarinya \’Yar Shekara 10

0
1091

Musa Muhammad  Kutama, Daga  Kalaba

ANA zargin  Dattijo mai kimanin shekara  61 da haihuwa mai suna  Timothy Onyeukwu, da boye wata karamar yarinya mai kimanin shekaru 10 da haihuwa yana holewarsa da ita a wani otel da ke garin Aba ,jihar Abiya na tsawon wasu watanni.

Da take gabatar wa manema labarai da wanda ake zargin tare da gungun wasu’yan fashi a hedkwatar rundunar .da ke Umuahiya rundunar ‘yan sandan jihar ta ce bayanan sirri da aka kyankyasa mata ne ya sanya ta kai ga nasarar kama wadanda ake zargin

kwamishinan‘yan sandan jihar Abiya  Adeleye Oyebade,ya ce “runduna ta tsakiya wato central ce da ke garin Aba ta yi kamen bayan da labarin maboyar masu laifin ya risketa. Haka nan kuma ya yi bayanin yarinyar an kai ta asibiti domin a  duba lafiyar ta”.

Da aka tambaye shi ko wanda ake zargi da yi wa yarinyar fyade ya amsa laifinsa, a nan ma kwamishinan ‘yan sandan ya ce da bakinsa ya yi ikrari ba tilasta shi akay i ba  ya aikata laifin da ake zarginsa da shi . “Ya tabbatar mana cewa hakika yana kwana da yarinyar a otel, na wasu tsawon watanni.”Ya kara da cewa da zarar sun gama bincike kotu za su gurfanar da mai laifin da ake zargi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here