Fulani Makiyaya Sun Jawo Hankalin Gwamnatin Jihar Imo

0
1200

Musa Muhammad  Kutama, Daga Okigwe.

WASU Fulani makiyaya mazauna garin Okigwe ,jihar Imo sun bayyana matukar takaicin su na  irin yadda wasu gwamnatoci a kudancin Nijeriya ke yada su , suna kiransu ‘yan ta’adda da kuma  bata  sana’ar su musamman ma irin yadda suke cusa kabilanci tsakanin al’ummar fulanin da kuma ‘yan asalin jihohin kudu maso gabas  da suke zaune alhali fulanin sun shafe shekaru masu tsawon gaske suna zaune a wadannan yankuna.

Wani mazaunin Okigwe mai suna Mugodi Musa da yake zantawa da wakilinmu na kudanci, ya ce sun shafe sama da shekara talatin da takwas suna zaune a Okigwe”kuma a nan ma aka haifemu muna son gwamnati ta taimake mu da abu biyu farko , makaranta ta boko da yaranmu za su rika karatu sannan kuma wurin zama namu na dindindin domin tun da aka rusa garke shekarun baya aka tashe mu tun da wurin na gwamnati ne amma kuma yanzu wannan gwamnati ta dawo da garken a samar mana da matsugunni ,tun da da can gidajen na gwamnati ne aka bari muna zaune amma an karbe ,muna son a samar mana da wuri da iyalanmu za su zauna yaranmu su rika yin karatu dabbobinmu suna kiwo abin da  muke bukata ke nan’’.

Da ya  juya kan batun samar masu da burtali ya yi na’am da yunkurin hakan matukar gwamnatin jihar Imo za ta yi masu hakan saboda zai saukaka masu wahalar tafiya kiwo da suke yi “daga nan muna tashi da shanunmu har zuwa Bayelsa,daga nan zuwa Fatakwal, ka ga  yanzu shanunmu yanzu wasu  suna Akwa Ibom ka ga idan an fidda mana da burtaloli ba mu da matsaloli, don wannan tsangwamar da ake yi mana ana cewa mu Fulani muna da kaza-kaza kamar yadda wasu gwamnatocin kudancin Nijeriya suke tsangwamar mu suna cusa wa al’umar su kabilanci hakan zai magance irin wadancan matsaloli da muke fuskanta a wasu yankunan kudancin kasar nan .

Shi ma Yunusa Abubakar  sarkin Gainakai, na garken kasuwar shanu ta Okigwe  da yake tofa albarkacin bakinsa yayin hira da wakilinmu kan hanyoyin da yake gani idan an bi su za a samu saukin kawar da rikici tsakanin makiyaya da manoma da ma magance shi,  cewa ya yi  “Fulani da manoma ai abokan zama ne domin saniya ba ta zama sai da  manomi amma hanyar da za a bi a warware rikicin shi ne shugabanni da iyayen kasa wato sarakunan gargajiya su daina sanya siyasa a ciki da kuma kabilanci idan har wata barna ta faru tsakanin makiyayi da manomi kamata ya yi a rika warware tat a hanyar lumana “.

Karshe ya bayyana zaman lafiya da mutunta juna tsakanin su da manoma ‘yan asalin jihar Imo babu wata matsala tsakanin su ya yaba irin  yadda gwamnan jihar yake bakin kokarinsa na ya ga an zauna lafiya tsakanin duk wani dan arewa mazaunin jiharsa da kuma tsakanin makiyaya da manoma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here