GWAMNA OBIONO YA SHA ALWASHIN GINA TITUNA 111 A WATANNI 3

  0
  890

  Daga Usman Nasidi

  GWAMNAN Jihar Anambra, Willie Obiano yace zai kammala gina tituna har guda 111 a fadin jiharsa cikin watanni uku rak.
  Gwamnan dai ya bayyana haka ne a jiya, Asabar 7 ga wannan wata.
  Gwamnan ya ce titunan za su yi amfani wajen harkar kasuwanci da noma.
  Gwamna Obiano ya ce kuma kowane bangare na jihar zai amfana da wannan aiki, watau dai babu inda ba za a shiga ba.
  Ana dai samun manyan motoci masu ratsa Jihar ta Anambra masu bukatar titi.
  Willie Obiao ya ce wannan shekarar fintinkau ce, ya ce Jihar Anambra za ta ga abin da ba ta taba gani ba a tarihi.
  Gwamnan ya ce jama’a sun gama shan wahala da kokawa game da tituna da sauran abubuwa.
  A kwanakin baya dai wani dan takarar kujerar Gwamna na Jihar Anambra, Cif George Moghalu ya roki jama’a su zabi jam’iyyarsu ta APC a zaben Gwamnan Jihar na Anambra da za a yi wannan shekarar.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here