Musa Muhammad Kutama Daga Kalaba
DUK da kasancewa ranakun mika takardun shiga takarar zaben shugabannin hukumar kwallon kafa ta Afrika wato CAF na kara matsowa zai yi wa hukumar kwallon kafar Nijeriya wuyar gaske ta maye gurbin shugaban hukumar ta kasar wato NFF Amaju Pinnick, .tun farko dai hukumar ta bayar da wa’adin 15 ga watan Disambar bara na kowane dan takara ya mika takardunsa amma shi shugaban an ruwaito ya mika nasa takardun ba tare da ya samu sahalewar sauran shugabannin hukumar NFF ba kamar yadda sauran shugabannin da suga gabace shi irin su Alhaji Aminu Maigari da Alhaji Ibrahim Galadima suka yi ba.
Shi dai shugaban hukumar kwallon kafar na Nijeriya bai samu yardarm gwamnati ba bare ta sauran makaraban hukumar . Ganin haka ne ministan matasa da wasanni Barista Solomon Dalung ya ce dole sai an kafa wani kwakkwaran kwamiti da zai zabo wani wanda ya cancanta da zai wakilci Nijeriya a hukumar ta CAF .
Zaben an tsayar da 16 ga watan Maris mai zuwa da za a yi a Ethiopia babban birnin kasar Habasha.