Jam\’iyyar APC Ba Ta Hausawa Ba Ce Ko Shugaba Buhari – Orji Kalu

    1
    1130

    Musa Muhammad Kutama Daga Umiahiya

    TSOHON Gwamnan jihar Abiya  Orji Uzor Kalu ya yi hasashen idan har ‘yan kabilar Ibo na son wani daga shiyyar kudu maso gabas da ya fito ya zama shugaban Nijeriya to su shafa wa kan su ruwa su shiga jam’iyyar APC yin hakan ne kadai zai sanya dan kabilar Ibon ya iya  zama shugaban kasa.

    Kalu ya yi wancan hasashe ne yayin da yake gana wa da shugabannin da suka ja ragamar gwamnatin sa suka kuma rike mukaman siyasa tare da shi lokacin yana Gwamnan jihar Abiya a kauyen  Igbere  yankin  Bende, da ke jihar.Ya ci gaba da cewa jam’iyyar APC ba ta Hausawa ba ce kuma ba ta shugaban kasa Muhammadun Buhari ba ce “don haka ina kira gare ku da ku shiga jam’iyyar APC bari in gaya masu gaskiya karara, wannan jam’iyya ba ta Hausawa ba ce ku daina bari ana rudin ku da wannan Magana, kuma hasashe ya nuna dan kabilar Ibo ya zama dan takarar shugaban kasa har ma ya shugabancin kasar nan karara sai a jam’iyyar APC ba PDP ba ko wata jam’iyya daban ba ta kasar nan ”.inji shi.

    Haka nan kuma ya yi tsokaci da lokacin da aka kafa jam’iyyar PDP babu irin abin da ba,a fada ba a ce jam’iyyar Hausawa ce kamar yadda a yanzu ake fada amma masu wancan rade-radi sun manta a PDP ce aka fitar da wadanda suka shugabanci kasar nan irin su Olusegun Obasanjo da kuma Goodluck Jonathan kuma duk kan su ‘yan kudu don haka ku fito ku yi siyasa ba ta bangaranci ko kabilanci ba .yana mai shawartar su.

    1 COMMENT

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here