An Cafke Wata Mata Da Ta Cutar Da Yaro Karami

0
967

Musa Muhammad Kutama, Daga Legas

RUNDUNAR ‘yan snadan Jihar Legas ta cafke wata mata mai suna Misis Bassey bisa zargin cusa tsinken tsintsiya a mazakuntar wani karamamin yaro mai suna Promise dan shekara 9 da haihuwa.

Bayanan da wannan jarida ta samu game ad wadda ake zargi ta zargi yaro Promise ne da yi mata satar kudi kudi Naira dubu 2 bayan ta sanya tsinken tsintsiyar a mazakuntar yaro ta nika barkono ta yi masa dauki da shi yaron na zaman dan kanenta da ta yi wa haka .

Majiyar labarinmu ta nuna cewa wanna abu ya faru a yanki Ebuta-meta na birnin Legas ne ranar Litinin da ta gabata majiyar mu taci gaba da cewa makwabta ne da suka ga azabtarwar ta yi yawa suka sanarwa hukuma daga nan kuma aka yi gaggawar kai yaron asibiti har aka yi nasarar cire tsinken tsintsiyar ..

.Wani babban jami’in ‘yan sanda da aka sakaya sunan sa ya ce  an kama Misis Bassey tana hannu shi kuma yaron yana samun sauki a asibiti tun da an cire  masa tsinken tsintsiyar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here