Jami\’an Tsaro Sun Damke Matar Da Ta Musanya Mataccen Jariri Da Mai Rai

0
790

Musa Muhammad Kutama, Daga Legas

JAMI’AN tsaro na rundunar ‘yan sandan jihar Legas,da ke Igbobo, yankin Ikorodu sun cafke wani magidanci mai suna  Jamiu Jimoh, tare da ‘yar aikinsa mai suna Yetunde Osin, wadda ke aikin karbar haihuwa a wani asibiti sakamakon zargin da ake yi wa Osin na sace jariri  lokacin da take taimaka wa wata mace da take yin  nakuda za ta haihu mai suna Stella,shekarar da ta gabata.Wadda ake zargi ta ce ba satar jaririn ta yi ba a’a ta gan shi ne a yashe karkashin gada .

Osin  da ake binciken ta ta  tsaya kai da fata  cewa ita ta samu jaririn ne a karkashin gada ita kuma daga nan sai ta dauko jaririn ta zo da shi gidan su “ni kuma ganin yaddda mutane suka sanya mi suna ta zunde na ya sa na dauki jaririn na kai shi gidan bababna a ikorodu”inji ta.

Ta ci gaba da gaya wa ‘yan sanda cewa ita mai karbar haihuwa ce fa ta yaya za a yi a ce ta saci yaro kuma ko da ‘yan sanda suka tambaye ta, ta shaida masu cewa ita ta karbi haihuwar Stella a watan shekaranjiya a asibitinsu. Jimoh mahaifin Yetunde ya shaida wa ‘yan sanda cewa shi bai san cewa jarirn satar sa aka yi ba.Bincike na ci gaba da gudana da zarar an gama za a mika ta gaban kuliya inji yan sandan.

‘Yan sanda na zargin Yetunde Jimoh ne da sace jaririn daga uwarsa bayan ta haihu ta musanya mata shi da wani matacce.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here