\’YAN MAJALISAR APC SUN TSIGE SANATA NDUME DAGA MUKAMINSA

  0
  842

  Daga Usman Nasidi

  AN cire Sanata Ali Ndume na Kudancin Borno a matsayin jigon majalisar dattawa yayin da wasu alamu masu tsanani suka bullo a ranar Talata, 10 ga watan Janairu, cewa rikicin cikin gida na jam’iyya mai ci ta All Progrssives Congress (APC) ya dauki wani sabon sauyi.
  A wani sako da aka aika zuwa ga majalisar dattawa a ranar Talata, Kusoshin APC sun mika sunan Sanata Ahmed Lawal na Arewacin Yobe a matsayin sabon shugaba a majalisar dattawa.
  A cewar kusoshin na jam’iyyar APC, an yanke hukuncin ne a lokacin taron kusoshin jam’iyya da aka yi a ranar Litinin, 9 ga watan Janairu.
  A halin da ake ciki, Ali Ndume ya yi watsi da cire shi da kusoshin APC suka yi a matsayin shugaba a majalisar dattawa.
  “Har yanzu ni shugaba ne a majalisar dattawa,” Ndume ya yi ikirin haka a lokacin taron manema labarai a majalisa a ranar Talata.
  Ya kara da cewa shi baida masaniyan cire shi da kusoshin jam’iyyar APC suka yi.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here