Musa Muhammad Kutama Daga, Kalaba
HUKUMAR kwallon kafa ta duniya FIFA ta fitar da jerin sunayen kungiyoyin kwallon kafa da suka yi fice na watan Janairun 2017.Kungiyar wasan kwallon kafa ta Super Eagles ta matsa gaba kadan daga matsayinta zuwa na 50 .sannan kuma kungiyar ce ta bakwai a Nahiyar Afrika .
Sauran kasashen Afrika da ke bin Nijeriya a baya su ne na Senegal, da Kwaddebuwa da kuma Masar,sauran su ne kasashen Tunisiya, Aljeriya kasar jamhuriyar Kwango.