Kungiyar Kwallon Kafa Ta Ifeanyi Uba Ta Daga Kofin Premier Na Kasa

  0
  907

  Musa Muhammad Kutama, Daga Kalaba

  KUNGIYAR wasan kwallon kafa ta Ifeanyi Ubah da ke garin Nnewi jihar Anambra ce  ta lallasa zakarar wasan Premier ta Nijeriya ta bana Enugu Rangers.Kuma ta lashe kofin charity na bana da aka gudanar a filin wasa na kasa da ke Abuja.

  Duk da kasancewa sai da  aka shafe mintuna casa’in babu kungiyar da ta samu sa’ar zura kwallo a ragar ‘yar uwarta aka sake kara mintoci sha biyar nan ma haka aka tashi karshe sai a bugun daga kai sai mai tsaron gida ne kungiyar Ifeanyi Ubah ta yi galaba da ci 4 da 3 a kan Enugu Rangers zakarun gasar Premier ta bana.

  Wannan nasara da kungiyar ta yi ya ba da mamaki saboda alkalin wasa ya kori Kojo Bah mai tsaron  baya na kungiyar saboda keta da ya yi wa kyaftin din Enugu Rangers Olamilekan Adeleye.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here