Eunisell Ya Bai Wa Ribas United FC Kyautar Naira Miliyan 10

    0
    820

     

    Musa Muhammad Kutama, Daga Kalaba

    KAMFANIN da ke yin riguna mai suna Eunisell da ke Legas  ya bai wa kungiyar wasan kwallon kafa ta Ribas United, da ke garin Fatakwal  kyautar Naira Milyan goma sakamakon bajintar da suka yi a kakar wasa da ta gabata .Shugaban kamfanin Rivers  Chika Ikenga.ne ya sanar da haka yayin gabatar wa kungiyar samfurin rigunan wasan da za su yi amfani da su a wasannin sun a gida da waje.

    A cewar  Ikenga shugaban kamfanin, ladar da aka ba su an ba su ita ne bisa kwazo da cancanta da bajintar da suka yi a kakar wasan kwallon kafa da hukumar shirya gasar ta Nijeriya wato NPFL ta saba shiryawa kowace shekara ce suka yi abin a zo a gani.

    Ribas united dai wadda  aka fi sani da Dolphins FC ta rikide ne zuwa Ribas United saboda daukar nauyin kungiyar da gwamnatin jihar ta yi ne.Bugu da kari da ma nasarar da suka samu a lashe zakarun rukunin yan hudu-hudu da suka yi a Inugu kwanan baya.

    Da yake bayyana dalilan su na ci gaba da goya wa kungiyar baya ko ana muzuru ana shaho Chika Ikenga ya ce “saboda kwazosu ba ma haka kadai ne ya sanya ba ko suna halin samun nasara ko akasi za mu ci gaba da tallafa masu”.inji shi,

    Daga karshe ya bayar da tabbacin kamfaninsa zai ci gaba da tallafa wa kungiyar Ribas United ta kowace hanya in dai a harkar wasan kwallon kafa ce.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here