Musa Muhammad Kutama, Daga Kalaba
FITACCEN jarumin fina-finan Hausa na Kannywood kuma mawaki Adam Zango zai cashe a kasar Kanada domin ya amsa goron gayyata da kasar ta yi masa yayin da take kokarin yin bikin cika shekaru 150 da zama kasa.
Wakilinmu na Kudanci ya ruwaito cewa, Adam Zango da kansa ne ya sanar da haka ta shafinsa na Instgram lokacin da ya sanar wa dimbin masoyansa ta shafin nasa sanarwar gayyatar da aka yi masa.
Ya ce idan ya je kasar zai yi bakin kokari ya ga ya kankaro sunan Nijeriya kasarsa ta gado da kuma daukaka martabar Arewa kamar yadda aka santa a sauran sassan duniya.Gayyatar kamar yadda aka ruwaito ya sanar zai cashe ne 14 ga watan Yuli na 2017 .Ya ci gaba da sanar da batun “yan Nijeriya ne mazauna kasar Kanada suka bukace da in je su ne suka gayyace ni na kuma amsa masu insha Allahu zan je kuma idan na je babu abin da zan yi sai in ga na kara daukaka martabar kasata Nijeriya da kuma Yyankina na Arewa kamar yadda aka sani”inji shi.
Ya kara da cewa a cikin takardar gayyatar sun ce sun yi “imani ni ne kadai zan iya daga darajar al’adu da martabar su kamar yadda na saba yi ta hanyar wakokina “don haka ne ma suka zabe ni suka kuma gayyace ni”.Cikin wata sanarwa ma da manajansa ya sanar ya yi bayanin sabgar ta kwana biyar ce za a yi kuma garurukan Ottawa, da Toronto, Ontario zai yi nasa wasan ne ranakun 13 zuwa 14 ga watan Yulin wannna shekara inji manajan Zango.