Eyimba FC Ta Lallasa Sunshines Da Ci Daya Mai Ban Takaici

  0
  828

  Musa Muhammad Kutama, Daga Kalaba

  KUNGIYAR wasan kwallon kafa ta Enyimba da ke Aba ta jihar Abiya wadda take yin wasanta na gida a Kalaba jihar Kuros Riba ta fara wasanta na makon farko a gasar wasannin kwararru na Nijeriya da kafar dama fafatwar da sukaji jiya Lahadi a filin wasa na UJ Esyene da ke Kalaba.

  Wasan kamar yadda aka saba an fara shi da misalin karfe hudu na yammacin ranar .Dan wasan gaba na kungiyar Enyimba mai suna  Ibrahim Mustapha ne ya zura kwallon a daidai minti na ashirin da fara wasan.Haka kungiyoyin biyu sukaci gaba da fafata wa suna ta kai wa juna hari, Enyimba na neman kara kwallo yayin da ita kuma Sunshines Akure ke kokarin farke kwallon da aka sanya masu cikin zare haka dai aka tafi hutun rabin lokaci Enyimba na da kwallo daya a raga ita kuma Sunshine s na nema.

  Bayan da aka dawo daga shakatawar rabin lokaci ne masu horas da kungiyoyin kowa ya rika sauya dan wasansa yana sanya zaratan da ya boye a benci Enyimba na neman kari yayin da ita kuma Sunshines ke neman farkewa har ta nemi kari amma haka aka tashi wasan Enyimba fc Aba nada kwallo daya  mai ban haushi a ragar Sunshines yayin da ita kuma Sunshine Stars da suka yo tattaki tun daga Akure jihar Ondo suka tashi a tutar babu suna nema.

  Babban mai horas da kungiyar ‘yan wasan kwallon kafa ta Akure Ale Olanriwaju ya shaida wa wakilinmu cewa kusakuren da ya jawo masu rashin samaun nasara na da nasaba da rashin kai hari da kuma kwace kwallo da ‘yan wasan gaba na kungiyarsa ba sa yi ne kana kuma “sabbin ‘yan wasa ne ba su gama gane junansu b a amma tun da mun ga inda barakar take za mu gyara kafin wasa na gaba”inji shi.

  Shi ma mai horas da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta enyimba Oluwandu Chibuzor yace “ai dama abin da muke fatar samu kenan nasara ga shi kuma ta samu muna fata karawar da za mu yi ranar Laraba  a Jos da kungiyar kwallon kafa ta Plateau United ma tarihi ya maimaita kansa.”inji  mai horas da Enyimba.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here