Makarantar Haddar Alkura\’ani Ta Madinatul Ahbab Kwaftara Ta ya ye Dalibai 66

0
919

Isah Ahmed Daga  Jos

MAKARANTAR koyar da haddar  karatun Alkura\’ani mai girma ta madinatul
ahbab da ke Kwaftara kusa da garin Saminaka da ke karamar hukumar Lere
a jihar Kaduna, ta yi bikin yaye dalibanta karo na 26 a inda ta yaye
dalibai  guda 66 a ranar Lahadin nan da ta gabata.
Da yake jawabi a wajen taron shugaban makarantun madinatul ahbab na
kasa Sheikh Falalu Dan Almajiri Fage Kano, ya bayyana cewa wannan yaye
dalibai wani babban abin farin ciki ne ga al\’ummar musulmin  duniya
baki daya.
Ya ce babban abin da suka sanya a gaba shi ne ilmintar da \’yayan
al\’ummar musulmi domin su fahimci ilmin addini musulunci da na zamani.
\’\’Don haka ya zuwa yanzu muna da  makarantu sama da 300 a sassa daban-
daban  na kasar nan. Daga cikin daliban da muka yaye akwai
wadanda suka zama Alkalai da malaman jami\’o\’i da likitoci da dai
sauransu\’\’.
Ya yi kira ga gwamnatoci da sauran masu hali su rika taimaka wa irin
wadannan  makarantu na haddar Alkura\’ani mai girma,saboda kokarin da
suke yi, na  fitar da matasa masu taimaka wa kasa da ci gabanta.
Ya ce daliban irin wadannan makarantu ba sa shaye-shaye da sace sace da
ta\’addanci. Don haka ya zama wajibi ga gwamnati ta rika taimaka wa irin wadannan makarantu.
Shi ma a nasa jawabin Talban Saminaka Alhaji Musa Mudi  ya bayyana cewa
yanzu dai kowa ya san muhimmancin ilmi, domin  babu wani ci gaba da za
a samu idan ba ilmi. Don haka ya yi kira ga al\’umma kan su bada
gudunmawarsu kan harkokin ilmi, domin \’yayanmu su sami ilmi, su zama
mutane  nagari.
Tun da farko a nasa jawabin daraktan Makarantun Madinatul Ahbab na
shiyar Saminaka, Malam Muhammad Akibu Salihu Kwaftara ya bayyana cewa
sun shirya taron ne don  yaye  dalibansu  da suka sauke Alkura\’ani mai
girma guda 56 da kuma wadanda suka sami hadda guda 10.
Ya ce daga lokacin da suka bude  wannan makaranta zuwa yanzu sun yaye
dalibai sama da guda 500.
Ya ce suna fuskantar matsalar rashin kudade da rashin ingancin
azuzuwanmu a wannan makaranta. Don haka ya yi kira ga al\’umma kan a
tallafa masu domin su sami damar  rufe azuzuwa guda 5 da suka gina a
wannan makaranta.
Daga nan ya yi ga gwamnati kan  ta gina masu rijiyar burtsatse a wannan makaranta.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here