Tafeeda Ya Gargadi Daliban Makarantar Madrasatu Kitab Was Sunnah

0
905

Zubair Abdullahi Sada, Daga Kaduna

SHUGABAN rukunonin JITA, Honorabul Jibril Lawal Tafeeda ya ja hankulan daliban makarantar Kitabu Was Sunnah da ke titin Gaskiya a Unguwar Sanusi, Kaduna kan su kula da karatunsu na fiyayyen littafi a doron kasa, wato Alkur\’ani mai girma da littattafan Hadisan Manzon Rahama, Muhammad SAW da na Fiqh, sa\’annan kaada su manta da neman ilimi na zamani, wato boko da ake kira \’Western Education\’ domin su cimma nasarorin da Arewa da kasar Najeriya ke bukata a fannoni da dama.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, wakilinsa na musamman a fannin tallafi na addini da wasu ayyuka, Alhaji Muhammad M.S ne ya fadi sakon na Jibril Tafeeda a lokacin da yake bai wa dalibai masu saukar Alkur\’ani da suka sami mafificin sakamako na daya da biyu da na uku a cikin dalibai 63 da suka sami sauke Alkur\’anin, inda ya damka masu kyautar Alkur\’ani mai girma da kudi dubu goma-goma su ukun.

Tafeeda ya ce, kalubale ne sosai a gare su, su daliban ilimi da su yi biyayya ga dokokin Allah da fadin Manzon Allah SAW, sannan su nemi ilimin boko domin samar wa rayuwarsu da na bayansu mafita daga kangin rashi da zaman kawai babu aikin yi. Ya gode wa mahukuntan makarantar inda ya ce, Allah ne Zai saka masu yadda suke kokartawa wajen tallafa wa karatun matasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here