An Gano Wani Bam Da Ya Yi Shekaru 40 Na Yakin Basasa A Ebonyi

0
1003

Musa Muhammad Kutama, Daga Kalaba

RUNDUNAR  ‘yan sandan Jihar Ebonyi ta ce an gano kwanson ragowar wani abu da ake zato kunshin bam ne da aka yi amfani da shi lokacin yakin basasar kasar nan na shekarun baya da suka wuce bai fashe ba.Kwanson bam din da aka ce wani dan bola jari ya gani, shi ne sai ya sanar wa da hukuma  a yankin  Okposi, karamar hukumar  Ohaozara ta jihar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa wani dan bola jari ne ya ga bam din da bai tashi ba wanda ya shafe shekaru 40 kenan tun lokacin yakin basasa da aka gama a shekara ta 1970.An kuma gan shi a  kauyen Onu Ezeukwu da ke karkarar.  .

Kakakin rundunar ‘yan sandan Ebonyi  DSP James Madu, ya sanar wa da ‘yan jarida cewa  “irin bama-baman da aka rika amfani da su ne lokacin yakin basasar kasar nan”ya ce an tafi da bam din Abuja domin masana kan harkokin abubuwan fashewa su yi bincike kansa ko yana da sauran karfi a jikinsa.

Jami’in ‘yan sandan ya yi watsi da rade-radin da ake bazawa cewa ‘yan boko haram ne suka dasa shi, kamar yadda jita-jita ta cika jihar an dasa bam kwanan baya lamarin da ashe ba gaskiya ba ne  inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here