MUSA MUHD.KUTAMA Daga Kalaba
HUKUMAR shirya gasar kwallon kafa ta Nijeriya LMC ta ci tarar kungiyar kwallon kafa ta Ifeanyi Ubah Naira Miliyan 9, .Ita dai kungiyar kwallon kafa ta IfeanyiUbah, ta hadu da fushin hukumar ce ranar Asabar a fafatawar da kungiyar ta yi makon farko na bude gasar wasan Premier a karawarsu da takwararta ta Kano Pillars a filin wasa na Sani Abacha da ke Kanon Dabo.
Tun farko kungiyar sun yi zargin alkaliyar wasa da ta hura wasan a lokacin da ki yi masu adalci a wani bugun daga kai sai mai tsaron gida da kungiyar ta samu amma suka yi zargin alkaliyar wasan ta ki ba su ,daga nan ne fa aka ce sai suka kaurace wa filin wasan bayan da aka dawo hutun rabin lokaci ‘yan wasan kungiyar suka ki yarda su dawo fili a ci gaba da wasa.
Gaskiya ta fi kwabo ta ruwaito bayan tarar ta Milyan tara da aka yi wa kungiyarm za su rasa maki uku da kuma yawan kwallaye uku duk a saboda halin rashin da,a da suka nuna yayin gasar ta makon farko da suka yi a Kano, kuma mata majiya kusa da kungiyar da ta bukaci a sakaya sunan ta ta jiwo mahukuntan kungiyar na cewa ba za su daukaka kara ba sun karbi hukuncin da hannu bibbiyu , sun rungumim kaddara.