Mustapha Imrana, Daga Kaduna
KWAMISHINAN \’yan sandan Jihar Sakkwato ya tabbatar da sace Daraktan kudi na karamar hukumar Isa da kuma wasu mutane uku.
Rahotannin da suke fitowa daga Sakkwato na cewa masu satar mutane sun sace mutanen ne a kan titin Sakkwato zuwa Isa a ranar Litinin.
Kwamishinan ya kara da cewa maharan masu dauke da bindigar da ba a san ko su waye ba suna rike da wadanda suka sace a Dajin Gundumi da ke a kasar Goronyo karamar hukumar Goronyo suna rike da mutanen.
Kwamishinan \’yan sandan ya ci gaba, \”tuni rundunar ta tura jami\’anta a cikin farin kaya da masu yunifom domin gudanar da bincike ta yadda za a zakulo bata garin\”.
Wadanda suka sace mutanen har yau ba su yi magana da iyalinsu ba ko rundunar \’yan sandan.
Kuma wadanda suka yi aika-aikar ba su nemi komai ba ballantana wata bukata musamman kudin fansa.
Kwamishinan \’yan sanda Abdulkadir, ya yi kira ga daukacin jama\’a da su taimaka da duk wani bayanin da zai kai ga samun nasarar kubutar da wadannan mutane.