Saleh Muhammad, Daga Yola
GWAMNATIN tarayyar Najeriya ta bada tallafin magunguna da wasu kayan aikin jinya da kudin ya haura Naira Miliyan 60, ga mutanen da harin kunar bakin wake ta shafa a garin Madagali ta Jihar Adamawa.
Da take gabatar da kayan magunguna ga gwamnatin jihar a madadin ministar lafiya, shugabar sashen kula da abinci da magunguna ta
ma\’aikatar lafiyar Misis Chukwuma Modupe Omatie, ta ce an kawo tallafin magungunan ne don nuna jin kai ga mutanen da harin kunar bakin wake ta shafa a jihar.
Misis Chukwuma ta kuma jajanta wa gwamnatin jihar da ma iyalan mutanen da harin kunar bakin waken ta shafa a madadin gwamnatin tarayyar kasar, ta yi addu\’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa ransu, da fatan samun sauki cikin gaggawa ga mutanen da suka samu raunuka a yayin tashin bama- baman.
Da yake maida kalami gwamnan jihar Umaru Bindow Jibrilla, ya yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa tallafin magungunan da goyon bayan da yake bai wa jama\’ar jihar da ma arewa maso gabas baki daya.
Ya kuma yaba da kawo karshen \’yan kungiyar boko haram, ya bada tabbacin cewa magungunan za su kai ga jama\’ar da abin ya shafa, kamar yadda tawagar gwamnatin tarayyar ta bukaci a yi.
Gwamna Bindow ya kuma bukaci \’yan Najeriya da su ci gaba da yi wa kasar da shugaba Muhammadu Buhari addu\’a, domin samun damar cika alkawuran da ya yi wa jama\’ar kasar.