Daga Usman Nasidi
MAJALISAR wakilan tarayya ta soki gwamnatin tarayya a kan rike kudin da ya kamata a bai wa majalisar shari’ar tarayya NJC.
Hanarabul Aminu Shagari mai wakiltar mazabar Shagari/Yabo ne ya gabatar da wannan batu a zaman majalisar wakilan tarayya.
Shagari ya yi magana a kan cewa bangaren zartarwa ta saki kudin da aka yi kasafi ga NJC a kasafin kudin 2016.
Ya ce rashin sakin kudin NJC suka ne ga kundin tsarin mulkin Najeriya, shi ya sa yake kira ga abokan aikin shi su goyi bayan wannan batu nasa.
\’Yan majalisar sun tattauna a kan wannan al’amari kuma sun yarda a kan cewa, Suna kira ga shugaban kasa ya umruci ma’aikatar da ta kamata ta saki kudin NJC da ke cikin kasafin kudin 2016, kana su umurci kwamitocin shari’a da kudi su tabbatar da cewa an yi amfani da kudin yadda ya kamata bisa ka\’idojin da suke a shimfide.
A ranar Laraba, 18 ga watan Janairu, majalisar ta tattauna a kan abubuwan da ya shafi iyalan \’yan sandan da suka rayukansu.