\’YAN SANDA BA SU DA DAMAR DUBA WAYAR JAMA\’A BA TARE DA IZINI BA

0
874

Daga Usman Nasidi

WATA jami’ar ‘yan sanda a Legas ta ce ‘yan sanda ba su da izinin binciken na’urar waya a yayin da suke gudanar da aiki saboda kowa na da abubuwan sirri a wayoyinsa.
Dolapo Badmos wadda ita ce jami\’ar dangantaka da jama\’a ta rundunar \’yan sandan a jihar Legas ta ce\’ ‘yan sanda Najeriya ba su da hurumin bincika wayoyin jama’a saboda mutane na da sirri dabban-dabban a na’urarsu.
Badmos ta bayyana hakan ne a cikin wata hirar talabijin na Linda Ikeji  da aka yi da ita, inda ta yi karin bayanin cewa ba daidai ba ne ga ‘yan sanda su duba na’urar wayar jama’a a lokacin da su ke gudanar da aiki.
A cewar ta, sai dai in har rundunar ‘yan sanda ta samu wannan izini, amma yanzu ba daidai ba ne duba wayoyin mutane.
Ta ce: \’Wayarka ita ce abin sirrinka, don haka ta shawarci jami’an ‘yan sanda da su nisanci duba wayar jama’a ba tare da izini ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here