Ana Amfani Da Jarirai Wurin Kai Hare-Haren Kunar-Bakin-Wake\’

0
1018

Rabo Haladu Daga Kaduna

GWAMNATIN Jihar Adamawa  ta yi gargadin cewa mata \’yan kunar-bakin-wake sun fito da wata dabara da tafiya da jarirai wajen kai hari domin ka da a gano su.
Wannan gargadin ya zo ne bayan wasu mata biyu sun kai hari goye da jarirai a garin Madagali na jihar ta Adamawa, kimanin kwanakki goma da suka gabata.
Kwamishinan watsa labaran jihar Ahmed Sajo wanda ya fitar da wannan gargadin ya ce wannan salo ne mai matukar hadari.
\’\’Mu babban abin da muke so yanzu shi ne a karfafa ayyukan tattara bayanan sirri irin na \’yansandan ciki saboda a gane irin wadannan miyagun da suka saje cikin al\’umma; Mu kuma muna fadakar da mutane cewa kowa ya bude idanunsa ya san makwabcinsa, ya san bakon da ya shigo gari.\’\’ In ji kwamishinan watsa labaran a cikin wata hira da manema  labarai
A ranar 13 ga wannan watan na Janairu ne dai wasu mata \’yan kunar-bakin-wake hudu suka kutsa kai cikin garin na Madagali.
\’Yan banga sun samu gane biyu daga cikinsu a wani wurin bincike kuma suka tsai da su kodayake bama-baman da ke jikinsu sun tarwatse nan take.
Amma sauran biyun sun samu wuce wurin binciken ba tare da an gano su ba domin an dauka fararen hula ne saboda suna dauke da jarirai.
Bayan sun wuce ne suka tayar da bama-baman da ke jikinsu a lokaci guda inda suka kashe kawunansu da jariran da kuma fararen hula hudu.
Sannanen abu ne dai cewa kungiyar Boko Haram na amfani da mata, wajen kai hare-haren kunar-bakin-wake; amma wannan shi ne karon farko da suka yi amfani da jarirai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here