Mata Miliyan Daya Za Su Yi Zanga-Zanga A Amurka

0
868

Wadansu mata miliyan daya ake saran za su yi zanga zangar kin jinin shugaban Amurka da aka rantsar da shi a jiya Juma\’a.

Su dai wadannan mata sun bayyana cewa za su hallara ne a cikin babban birnin Washington mazaunin gwamnatin kasar domin ci gaba da nuna kin jinin mista Donal Triumph da ya kama aiki a matsayin shugaban Amurka na 45.

Ko a jiya dukkan harabar dandalin da aka rantsar da sabon shugaban na Amurka sai da tarzoma ta barke inda aka faffasa motoci da shaguna har da kunna wuta duk domin kin jinin shugaban na Amurka da ya sha rantsuwar kama aiki a jiya Juma\’a.

Da akwai wani birnin da mutane dubu uku suka kama hannun juna suna rera wakokin kin jinin shugaban har wasu na fadin wannan masomin abin da suke kokarin yi ne koda yake ba a ma fara ba.

Abin jira a gani dai shi ne irin yadda al\’amarin zai kasance idan an jima kadan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here