Mene Ne Ya Sa Shugaba Buhari Ya Sake Tura Sunan Magu Majalisa?

0
1223

Rabo Haladu Daga  Kaduna

SHUGABAN kasa Muhammadu Buhari ya sake tura sunan Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar da ke yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFFC zuwa majalisar dokokin kasa.
Ko da yake dai ba a bayyana hakan a hukumance ba, sai dai wani babban jami\’in gwamnatin ne ya shaida wa manema labarai  hakan.
A watan da ya gabata ne majalisar ta ki amincewa da tabbatar da nadin Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar ta EFCC, bayan wani rahoto da \’yan sanda da ake zarginsa da cin hanci da keta dokokin aiki.
Haka kuma, masu fafutuka sun ce majalisar ta ki amincewa da nadin nasa ne saboda yadda yake tsaya wa manyan \’yan siyasa masu hannu dumu-dumu a cin hanci.
Mista Magu ya kai kusan shekara daya yana shugabancin riko a hukumar EFCC.
An dade dai ana kai ruwa rana game da batun tabbatar da Mista Magu kan mukamin nasa.
Wannan ne dai karo na biyu da shugaba Buharin ya mika sunan Ibrahim Magu ga majalisar domin tabbatar da shi shugaban hukumar ta EFCC.
To ko mene ne dalilin da yasa shugaban yake son ganin majalisar ta amince da nadin Mista Magu?
Watakila Shugaba Buhari ya sake mika sunan Ibrahim Magu ga majalisar dattawan ne sakamakon binciken da ya kammala kan zargin da aka yi masa na aikata ba daidai ba.
Da ma dai shugaban ya bukaci ministan Shari\’a ya binciki wasu jami\’an gwamnatinsa, wadanda ake ganin sun hada da shi Ibrahim Magu bayan wani rahoton da hukumar leken asiri ta farin-kaya, DSS ta mika mata cewa shugaban na EFCC na da tabo a jikinsa.
Kazalika wasu na gani shugaba Buhari ya sake mika sunan Ibrahim Magu ga majalisar ne domin tabbatar masa da mukaminsa saboda sukar da akasarin \’yan kasar da ke ganin ana yi masa bi-ta-da-kulli kan yakin da yake yi da cin hanci da rashawa suka rika yi bayan majalisar ta ki tabbatar masa da mukamin nasa.
Masana kan yadda ake yaki da cin hanci a Najeriya dai na ganin tabbatarwa Magu wannan matsayi zai karfafa masa gwiwa a yunkurin da yake yi na kawar da wannan babban bala\’i da ya zamewa kasar tamkar cutar daji.
Wasu \’yan kasar da dama na ganin cewa Mista Magu ne ya fi cancanta da wannan matsayi saboda kokarinsa wajen yaki da cin hanci
A watan Disambar da ya gabata ma wasu \’yan Najeriyar suka bai wa \’yan majalisar dattawan kasar wa\’adin mako biyu da su tabbatar da Ibrahim Magu, a matsayin shugaban hukumar EFCC ko kuma su yi zanga-zanga a mazabun \’yan majalisar.
Inda suka ce duk wani yunkurin hana tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin shugaban EFCC na din-din-din zai iya yin zagon-kasa a yakin da Shugaba Muhammadu Buhari ke yi da cin hanci da rashawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here