\’Yan Gudun Hijira 10 Sun Samu Tallafin Karo Ilimi Na Kamfanin Sarrafa Iskar Gas A Adamawa

0
866

Muhammad Saleh, Daga Yola
KAMFANIN sarrafa iskar gas na kasa (Nigerian Gas Company) ya samarwa yara ‘yan gudun hijira 10 guraben karo ilimi a kwalejojin gwamnatin tarayya dake jihohin Adamawa, Gombe da Bauchi.
Da ya ke mika takardun shaidar samar da guraben karo ilimin ga yara ‘yan gudun hijiran, shugaban cocin Catholic da ke Yola Bishop Stephen Dami Mamza,  ya bayyana lamarin da cewa wata damace yaran suka samu daga Allah.
Ya ce wani alheri da ko dama da mutum zai samu zai mishi wuyar samu har ya amfana dashi in ba albarkacin raba shi da muhallansu da ‘yan kungiyar Boko Haram suka yi ba.
Bishop Dami Manza ya bayyana yadda za’a kashe wasu daga cikin kudaden da cewa za a biya kudi makaranta da abinci, kiwon lafiya inifom, gusiri hadi da sufurin iyayen yaran ta yadda za su samu sukunin ziyartar ‘ya’yansu a makaranta.
Wasu daga cikin yaran da suka amfana, Elijah Bitrus da Susana Luka sun nuna farin cikinsu tare da fatan za su zama likita da lauya bayan sun kammala karatun.
Haka suma wasu daga iyayen yaran da suka amfana da tallafin sun godewa kamfanin dama cocin Katolika da damar da suka  bai wa \’ya’yansu abin da suka bayyana da ba su tava tsammani a rayuwarsu ba.
Cocin Katolika da ke Yola yana daukan nauyin karatun yara ‘yan gudun hijira sama da dubu biyu dari biyar daga matakin firamare zuwa gaba a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here