KUNGIYAR yan asalin kasar Nijar mazauna Kaduna ta tsakiya tare da hadin gwiwar Idris Dan bushiya na shirye shiryen fara gudanar da gasar kokawar gargajiya domin lashe mota da sauran kyaututtuka a Kaduna.
Kamar dai yadda Idris da kuma Laminu kakakin kungiyar yan asalin kasar Nijar mazauna Kaduna suka shaidawa wakilinmu a garin Kaduna cewa a karshen wannan watan ne 30/1/2017 za a fara gasar a filin kokawa da ke ungiwar Dan bushiya cikin garin Kaduna.
Duk sun bayyana cewa suna son bunkawa tare da kara karfafa dankon zumunci a tsakanin al\’umar kasar Nijeriya da Nijar wadda kowa ya Sani cewa an Dade ana zaune tamkar uwa daya uba daya.
Sun kuma bayyana cewa suna Neman yan wasan kokawar daga ko ina suke a fadin duniya.
Kamar yadda suka shaidawa wakilin jaridar garkuwa a Kaduna cewa sun kammala shirya wa yan wasan wurin da za su zauna da dai Samar da kayan bukatu.
\”Mun yi shirin samar da tsaro a lokacin gasar ta kokawa, Wanda hakan yasa muka gayyaci sarkin gasar kokawar kasar Nijar Wanda ya lashe Takobi a gasar da aka yi kwanan baya\”.
Idan hali ya yi zamu kawo maku sunayen yan wasan da ake saran su halarci gasar domin fafatawa.