Saleh Muhammad, Daga Yola
BAYAN kwashe shekaru uku da rufe sansanin horas da matasa ma su yiwa kasa hidima (NYSC) a jihar Adamawa sakamakon matsalar tsaro, yanzu hukumar ta sake bude sansanin.
Da yake magana da manema labarai a Yola, ranar talata Kodinetan hukumar NYSC a jihar Muhammed Abubakar, ya ce kimanin matasan 2, 500 za su gudanar da aikin yi wa kasa hidima a jihar.
\”Mun fara gudanar da rigistar matasan misalin bakwai na safe, ga shi kana gani matasan suna ta shigowa, muna tsammanin 2, 500 matasan za su shigo\”.
Shugaban hukumar ya ce an kuma samar da ingantaccen tsaro, domin kuwa ya ce akwai sama da jami\’ai 300 kama daga sojoji da \’yan sanda da jami\’an tsaron ciki (DSS) da masu farin kaya (NSCDC) da dama wasu jami\’an matasan NYSC.
Ya kuma yaba da kokarin gwamnatin jihar na samar da makarantar kimiyya da fasaha mallakin jihar (SPIY) a matsayin sansanin matasan na wucin-gadi kafin a kai ga kammala kwashe \’yan gudun hijira da suke zaune a sansanin matasan na dindindin da ke Damare cikin karamar hukumar Girei.
\”Ina son matasan su fahimci cewa wannan sansanin mun samar da shi aro ne, wanda kuma an samar da duk abubuwan bukata a ciki\” inji Abubakar.
A lokacin da yake yaba wa gwamnatin jihar bisa goyon bayan da ta ba su, shugaban ya kuma bukaci jama\’ar jihar da su ci gaba da bada goyon baya da kuma nuna jin-kai ga matasan masu yi wa kasa hidima a jihar.