Dubban Jama’a Ne Suka Canza Sheka Zuwa Jam’iyyar APC A Abiya

  0
  917

  MUSA MUHD KUTAMA, Daga Kalaba

  A Jihar Abiya mutane sama da dubu dari ne suka shiga jamiyyar APC inji shugaban jam’iyyar  Donatus Nwamkpa,ya ce cikin kwanaki goma kacal aka samu wannan tururuwar kuma galibin su daga kananan hukumomi goma sha bakwai da ake da su na jihar ne.

  ‘Mu burinmu ma mutane sama da dubu 300 muke sa rai su shigo jam’iyyar Apc amma wadan nan ma da aka samu mungode,ragowar ma muna sa rain an ba da jimawa ba za su shigo jamiyyar”inji shi. Ya kara da cewa harv yanzu kofar APC a bude take ga duk wani waada yake son yin kaura daga jam’iyyarsa ya dawo APC.

  Da yake yin tsokaci game da dawowar su jam’iyyar tsohon dan kwamitin amintattu na jam’iyyar day a baro  Benjamin Apugo, ya ce shida daukacin magoya bayan su ne da suka fuskanci rashin adalcin da ake masu ne ya sanya suka baro wacccan jam’iyya suka dawo APC  wasu kuma daga yankin Nkata Ibeku ,babban birnin jihar Umuahiya.

  Jagoran wadanda suka yi kaura da jam’iyyar PDP  na Jihar Sanata Chris Adighije, ya ce sun dawo jam’iyyar ce domin su kwace ta daga hannun jam’iyya mai mulkin jihar wato PDP zaben 2019 idan Allah ya kaimu .Wakilinmu ya ruwaito wadanda suka dawo din ‘yan jam’iyyar PDP ce mai mulkin jihar.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here