NPFL TACI TARAR ABIYA WARRIORS NAIRA N250,000

    0
    939

    MUSA MUHD .KUTAMA, Daga Kalaba

    HUKUMAR shirya gasar wasannin rukuni na kwallon kafa ta Nijeriya wato LMC, ta ci kungiyar wasan kwallon kafa ta Abiya Warrirors tarar Naira Dubu dari biyu da hamsin bayan da kungiyar ta fafata da takwararta ta  Abia Warriors ta Remo Stars sakamakon nuna halin rashin da’a da ‘yan wasan suka yi inda Remo Stars suka casa su da ci daya mai ban haushi .

    Bayanan da Gaskiya Ta Fi Kwabo  ta samu wato takaddama ce ta faru tsakanin kungiyoyin biyu sakamakon samun bugun daga kai sai mai tsaron gida da Remo Stars ta samu wanda sanadin hakan ya sanya ta yi galaba a kan Abiya wannan  lamari ne aka ce bai yi wa ‘yan wasan dadi ba suka harzuka suka tayar da boren kin shiga fili su ci gaba da yin wasa.

    Haka nan kuma an ruwato hukumar alkalan wasanni ta sanar da dakatar da wani alkalin wasa mai suna Dankano Abdullahi daga yin alkalancin wasa saboda zargin da ake masa nan  badakala a alkalancin wani wasa da ake zargi ya aikata har sai an gama binciken kan zargin da ake masa.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here