Sun Nemi Gwamnatin Kuros Riba Ta Saki Kudi Don Kammala Gyaran Filin Wasa Na Eyimba

  0
  828

  MUSA MUHD KUTAMA, Daga Kalaba

  KAMFANIN da ke kwantaragin gudanar da ayyukan gyara filin wasa na kungiyar kwallon kafa ta Enyimba da ke Aba, Jihar Abiya, mai suna  Moni Michelle, ya ce matukar gwamnatin jihar na son aikin gyara filin wasan ya ci gaba kuma ya yi armashi dole fa sai ta saki kudi da kamfanin zai ji dadin gudanar da aikinsa cikin sauri ya yi ya gama .

  Daraktan kamfanin da ke yin aikin  Ebi Egbe, ya sanarda haka ga manema labarai ya ce “jinkirin ba mu kudin da za a ci gaba da yin aiki da gwamnati take yi shi zai kawo mana tsaiko a aikinmu filin wasa ne babba mai daukar yawan ‘yan kallo dubu 25 amma gwamnati sai nuku-nuku take yi taki ta ba mu wadatattun kudi da za mu ci gaba da yin da zai sanya mun gama masu filin su dawo su ci gaba da amfani dashi amma an ki”inii shi.

  Daraktan kamfanin ya ci gaba da cewa tun fa “a shekara ta 2015 ne aka ba mu kwangilar yin aikin amma a ba mu isassun kudi da za mu yi aikin mu gama mu tafi an k. Ina kira ga gwamnatin Abiya da ta saki kudi ko mun kammala aikinmu mu san inda dare ya yi mana tun farko an shirya wasan gasar cin kofin Nahiyar Afrika a filin wasan kungiyar za ta yi amma ina har shekarar da ta gabata ba a mo ba labari na kammala aikin saboda kin ba mu kudin aiki”inji shi.

  “MoniMichelle ya ci gaba da cewa tun daga lokacin da ya rika jawo hankalin gwamnatin jihar ga shi saura baifi wata biyu ba a gama aiki amma wasa-wasa ana neman shekara ta biyu kenan ana abu daya ga farashin musayar kudaden kasar waje ya tashi idan aka kwatanta da yadda muka fara aikin a shekarar bara waccan .Saboda jinkirin kammala gyaran filin wasan yanzu haka kungiyar Enyimba Aba ta Kalaba Jihar Kuros Riba suna yin wasannin sun a gida kakar wasa ta bana .

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here