MUSA MUHD.KUTAMA, Daga Kalaba
‘YAN sandan Jihar Enugu sun kama wata mata mai suna Chinedu Chukwu, bisa zargin hada baki a sace ‘yar kanenta ta sayar kan kudi naira 350, 000.Haka nan kuma wacce ake zargin inji ‘yan sandan ta hada baki ne da saurayinta mai suna Osunkwo Chinonso suka sayar da yaron dan shekara hudu da haihuwa mai suna Chinecherem Irechukwu, dalibi a wata makarantar firamare da ke Enugu.
Kakakin rundunar ,yan sandan Ebere Amaraizu ya shaidawa wannan jarida ,cewa cigiyar bacewar Chinecherem Irechukwu, iyayen dake kauyen Inyi yankin karamar hukumar Oji river suka kawo wa rundunar ce daga nan kuma suka bazama nema kafin daga bisani a gano yadda aka yi har aka kai ga kama ita wadda ake zargin kuma tayi masu gamsassshen bayani yadda aka yi har hakan ta afku ba wani ya matsa ta ba .inji shi.
Jami,in yan sandan ya kara da cewa ta fadi mana cewa “ita da saurayintaOsunkwo sukaje makarantar da yarinyar take karatu tun daga Jihar Anambra suka je suka kirawo ta suka rude ta da kayan makulashe suka tafi da ita zuwa garin umuahiya wani kauye mai suna Olokoro suka sayar da ita ga wata mata mai fataucin yara mai suna Nwokocha Florence.kan kudi naira dubu 350.Ita kuma mai saye ta tsaya a layin Faulk dake garin Aba tana jiran masu zuwa su saya a hannunta daga nan ne kuma aka kubutar da yarinyar