MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba
WANI magidanci mai suna Ogundare, dake zaune a yankin Meiran , na Ebijimi birnin Legas ya kona farkarsa mai suna Oriyomi Folarin da saurayinta mai suna Akinade Omole,kafin hakan ya kasance ance masoyan biyu suna dasawa babu wata matsala tsaknin su ance shi wanda ake zargi da kona farkartasa da saurayinta nema ya kama mata daki da kuma shago tana kasuwanci a yankin Ogbado jihar Ogun take zaune .
Yadda hatsaniyar ta samo asali kamar yadda wata majiya ta shaidawa wakialinmu shi saurayin ne akace Ogundare ya hango shi ya ajiye motarsa mai tsada a wani wuri ya tafi shagon farkar tasa shi kuma daga nan sai ya yi wuf ya samo man fetur ya yi sanda ya watsa masu ya kyasta ashana ya jefa masu lamarin da ya yi sanadiyyar mahaukaciyar gobara da ta lakume rayukan farkar da saurayin nata .
Mai magana da yawun rundunar ,yan sandan Jihar Legas SP Dolapo Badmos, ya tabbatar da afkuwar lamarin sai dai kuma yace Ogundare zakara ya bashi sa,a amma kuma rundunar tasha alwashin duk inda ma ya je ya buya zata kama shi.