MATASA 2 SUN HALLAKA A WANI RIKICIN MATASA A KADUNA

0
1016
Daga Usman Nasidi

AKALLA Mutane biyu ne su ka sheka lahira sakamakon wata takaddama data kaure tsakanin matasan Unguwar Shanu da na Unguwar Sarki, dake makwabtaka da juna a cikin birnin jihar Kaduna.

An somo rikicin ne a lokacin da matasan Unguwar Shanu ne suka kai wani hari wanda ake kira da suna ‘shara’ a yankin Unguwar Sarki da misalin karfe 9 na daren Litinin.

Sai dai hausawa na cewa ‘kaikayi koma kan mashekiya’ sai ga shi an jikkata matasan unguwar shanun har su hudu, da suka hada da Tasiu Abdulahi, Yusuf Garba, Abdulahi Sani da Nasiru Lawal.

Sarkin Unguwar Shanu, Malam Aliyu Gumi ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace a yanzu haka sun rigaya sun binne Tasiu Abdullahi da Yusuf Garba, mutum biyu da suka rasa rayukansu yayin fadan.

Sarki Aliyu Gumi yace “labarin daya zo mana shine, matasan Unguwar shanu ne suka kai farmaki Unguwar Sarki, inda aka kashe mutane biyu, sa’annan aka jikkata mutane biyu, wanda a yanzu haka daya na hannun yansanda, daya kuma na asibitin Barau Dikko.”

Yayin da muka tuntubi hukumar yan sanda, Kaakakin hukumar ASP Aliyu Usman ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma yace suna cigaba da gudanar da bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here