Sheikh Muhammad Rabi\’u Daura Malamin Tauhidi Ne

0
2439

Daga Zubair A Sada

\’\’ SHAHARARREN malamin Sunnah da ke Kaduna, Sheikh Muhammad Rabi\’u Aliyu Daura babu abin da za mu ce a kan sa sai dai Allah Ya karbi bakuncinsa ya hada mu da shi a gidan Aljanna Firdausi. Ya yi rayuwarsa mai kyau daga fadakarwa da gudanar da tafsiri da wa\’azi babu abin da yake yi a cikin shekaru fiye da arba\’in a nan Kaduna\’\’.

Sheikh Sani Yahya Jingir ne ya yi wannan bayani a lokacin da ya jagoranci tawagar hadaddiyar kungiyar Izala ta kasa Jos da suka zo ta\’aziyyar rasuwar daya daga cikin dattijan Izalar, Malam Rabi\’u Daura wanda Allah Ya karbi rayuwarsa ranar Juma\’a kuma aka yi masa janaza ranar Asabar.

Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ce, Malam kodayaushe ba ya mantawa da batun tauhidi a dukkan lokacin da yake gabatar da wa\’azi ko nasiha a dukan tsawon rayuwarsa. Ya ce, duk malamin da kuka ga yana makale da tauhidi to, ko shakka babu babban mutum ne da ba shi tsoron komai ko kowa a duniya sai Ubangijinsa.

Ya yi addu\’ar Allah ya gafarta masa ya sanya aljanna makomarsa, su kuma iyalai Allah ya ba su hakurin wannan rashi. Ya kuma gargadi \’ya\’yan da ya bari da su ci gaba da yi wa kannen malam din biyayya da gudanar da zumunci a tsakaninsu, kada su yadda su yanke ko katse zumunci tsakaninsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here