Gidaunuyar T.Y. Danjuma Za Ta Tallafa Wa Jama\’ar Da Rikicin Boko Haram Ta Shafa Da Naira Biliyan Uku

0
848

Muhammad Saleh, Daga Yola

GIDAUNIYAR TY Danjuma mai aikin tallafa wa jama\’ar da rikicin boko haram ya shafa (Victims Support Fund) ta tsara yadda za ta kashe
kimanin Naira Biliyan uku a yankunan da rikicin yafi shafa a arewa maso gabashin Najeriya.
Da yake jawabi a wani taron masu ruwa da tsaki a Yola, shugaban gudanarwar gidauniyar Dokta Sunday Ocheche, ya ce gidauniyar za ta bude sabon ofishin yanki domin gudanar da aikin jinkai ga jama\’ar da bala\’in boko haram ta shafa.
Ya ce gidauniyar za ta kashe naira miliyan dubu talatin wajan tallafawa jama\’ar da rikicin ta shafa a jihohin Borno, Adamawa da Yobe a cikin wannan shekara ta 2017.
Ya ci gaba da cewa a kokarin sauke nauyin da ya rataya mata, Victims Support Fund  za ta bude ofisoshi a Yola da Maiduguri a farko farkon
watan na wannan shekarar.
Ya ce \”yanzu da yaki da \’yan bindigar boko haram ke kawo karshe, muna bukatar goyon baya da hadin kai masu ruwa da tsaki daga bangarori daban-daban domin cimma manufar tallafa wa jama\’ar wannan yankin kai tsaye\” inji Dakta Ocheche.
Shi ma shugaban gidauniyar Janaral TY Danjuma, (mai ritaya) wanda Ambasada John Gana, ya wakilta ya jaddada matsayar gidauniyar VSF na taimaka wa rayuwar jama\’ar da rikicin boko haram ya shafa a arewa maso gabashin kasar.
Tun da farko da yake bude taron na yini uku, mataimakin gwamnan jihar Martins Babale, ya ce irin matakan da gidauniyar ke dauka abin a yaba ne, ya ce a shekaru bakwai na rikicin boko haram gwamnatin jihar ta takarawar gani wajen inganta rayuwar \’yan gudun hijiran da suka fito daga kananan hukumomin jihar bakwai na jihar da ma na jihohin Borno da Yobe.
Taron ya samu halartar wakilai daga jihohin Borno da Yobe, inda suka yaba da kokarin gidauniyar na ganin ta tallafa wa rayuwar jama\’ar da
rikicin boko haram ta shafa a jihohin uku.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here