Muhammad Saleh, Daga Yola
WASU kungiyoyin taimakon kai-da-kai da suka hada da Janna Health Foundation da Best Agenda da hadin gwiwar Gidauniyar tallafa wa
mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa da Janar T.Y Danjuma, ke jagoranta suna tallafa wa marayu 150 da Naira Dubu goma sha hudu duk wata a Adamawa.
Tallafin da kungiyoyin suka bayar ga yara marayun ‘yan kasa da shekara sha biyu, an damka ne a hanun wasu iyalai saba’in da biyar, da suka
amshi amanar kula da marayun a garin Mayo-Konkol da ke karamar hukumar Maiha a jihar Adamawa.
Kungiyoyin suka ce an tsara shirin ne domin tallafa wa marayun ta hanyar ilimantarwa, kula da lafiya da ma tarbiyantar da marayun na
tsawon shekara guda, wanda ya fara aiki tun cikin watan Nuwambar shekarar 2016.
Dokta Abdullahi Belel shi ne shugaban kungiyar Janna Health Foundation, ya ce \’\’marayu 150 da aka tantance akwai gidaje 75 da za su kula da su na tsawon shekara guda. “A yau za a bada kudin wannan watan, amma mu mun fara tun cikin watan Nuwanbar 2016, mutanen Maiha sun yi abin da ya dace muna fata za su ci gaba da taimaka wa har wannan shirin ya kai ga nasara”.
Tun da farko dai kungiyoyin sun kuma shirya yin amfani da sarakunan gargajiya, malaman addini da kuma jami’an sashin kula da rayuwar
jama’a na karamar hukumar ta Maiha, wajen tantance iyalan da aka danka wa alhakin kula da marayun.
Shi ma da yake jawabi a taron shugaban kungiyar Best Agenda Alhaji Ahmed Lawal, ya shawarci iyayen da suka dauki amanar kula da marayun da cewa Allah zai tambayesu ya ce su yi amfani da wannan dama wajen samun rahmar Ubangiji.
Ya ce duk wanda Allah ya ba shi nauyin aikin kula da maraya tamkar gwajin karfin imanin mutum ne Allah ya’yi mishi, saboda haka ya
shawarce su da su kauce wa nuna banbanci tsakanin yaran da ya’yansu. “Ku kula da amanar kula da marayun nan kamar ya’yanku ku sani Allah zai tambaye ku amanar da kuka dauka kada ku nuna musu banbanci da \’ya’yan da kuka haifa ku rike su tamkar ku kuka haife su” inji Ahmad Lawan.
Muhammad Abba daya daga cikin iyayen da suka dauki amanar kula da yara marayun ya yaba da matakin da kungiyoyin suka dauka ya ce lamarin zai taimaka wajen kyautata rayuwar marayu a yankin.