Wasu Ma\’aikatan UN Biyar Sun Rasa Ransu A Kan Iyakan Kamaru da Najeriya

0
872

Muhammad Saleh, Daga Yola

MA\’AIKATAN kungiyar hadinkai kasashen Turai (UN) biyar sun rasa ransu a garin Koncha, lokacin da suke aikin shata iyaka tsakanin kasashen Najeriya da Kamaru.
Ma\’aikatan sun ziyarci yankin ne domin aikin tantance iyakokin kasashen biyu, wasu da ake jin barayi ne su ka kai mu su hari, kamar
yadda kwamishinan ma\’aikatar shari\’a ta jihar Baresta Silas Sanga, ya shaida wa manema labarin a Yola.
Ya ce an gama shirin tura sauran ma\’aikatan jihohin da suka fito dama wadanda su ka fito daga wasu kasashe na daban.
Ya ce an kuma tantance wasu daga cikin ma\’aikatan da suka rasa ransu da kasashen da suka fito, ya ce akwai mutanen kasashen Kenya da
Kamaru, sai kuma wadanda suka fito daga jihohin Adamawa, Jigawa da kuma Kano.
Kwamishinan da ya ce ba a kai ga tantance wadanda suka kai wa ma\’aikatan hari ba, amma dai ma\’aikatan sun tafi yankin aikin shata iyaka
tsakanin Najeriya da Kamaru ne, a garin Koncha maharan suka kai musu harin.
Wasu rahotannin da suke fitowa daga yankin sun yi zargin wasu jami\’an tsaron kasar ta Kamaru, suka harbe ma\’aikatan a garin na Koncha da ke kan iyakan Kamaru da karamar hukumar Toungo a jihar Adamawa.
Tuni dai wata tawaga karkashin mataimakin gwamnan jihar Martins Babale, ke aikin ganin ta tura sauran ma\’aikan da abin ya shafa inda
ya dace.
Ma\’aikatan dai sun tafi yankin ne domin aikin shata iyaka biyo bayan hukuncin da kotun kasa-da-kasa ta yanke na cewa kasar Najeriya ta mika yankin Bakassi ga kasar Kamaru a 2002.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here