Mustapha Imrana, Daga Kaduna
MAI shari\’a Adeniyi ya bayyana cewa sun yanke wa wadansu jami\’an sojan Nijeriya hukuncin dauri sakamakon aikata laifuka daban-daban da suka saba wa dokar aiki.
Mai shari\’a Adeniyi ya bayyana cewa a zaman da suka yi a Maiduguri sun samu Hassan Adamu da aikata laifin kisa ba da gangan ba don haka a madadin daurin rai da rai an yanke masa hukuncin shekaru 7 a Gidan yari saboda kashe Umar Akar da Hassan ya harbe shi da bindiga a kirji sau uku.
Hassan Adamu Wanda ya kasance kurtun soja ne sun samu takaddama tsakaninsa da Umar Ankar a ranar 23 ga watan Disamba 2014.
Tun da farko Lauyoyin Hassan Adamu sun yi jayayyar cewa ba da gangan ya kashe Umar Ankar ba domin Hassan ya yi kokarin kare kansa ne don haka ba da gangan ya aikata kisan ba.
Sai kuma wani kurtun soja shi ma mai suna Ebechi Eze da ya bace tsawon watanni 10 lokacin da aka tura su aiki a garin Goza.
Eze ya bayyana cewa Yan Boko Haram ne suka kama shi amma daga baya ya kubuce.
Amma duk da haka mai shari\’ar ya yanke masa hukuncin watanni 14 a Gidan maza
Sai dai an yi watsi da batun bacewar bindigarsa da harsasan da yake tare da su lokacin da abin ya faru.
Kuma mai shari\’ar ya ce duk hukuncin zai tabbata ne da amincewar rundunar sojan Nijeriya.
Barista Muhammed Umar sakataren kungiyar lauyoyin Jihar Borno ne ya bayyana gamsuwa da irin hukuncin da aka yanke da ya ce da ba a samu Umar da Hassan sun yi kokawa ba a kasuwar Litinin a garin Maiduguri da an yanke wa soja Hassan hukuncin kisa.
Wani babban soja Manjo Y Galadima, cewa ya yi yana son mutane su gane cewa da zarar an yankewa soja ko ofisa hukunci to an kore shi daga aiki kenan.