Ana Sa Ran Cimma Yarjejeniya Tsakanin Manoma Da Barayin Shanu

0
963

Mustapha I Abdullahi Kaduna

BAYAN da aka samu matsalokin kai ruwa rana da a karshe ya zama tilas ya zuwa yanzu an fara shirin kammala cimma yarjejeniya tsakanin manoma da wadanda ake zargin barayin shanu ne.

Wannan yunkurin cimma yarjejeniya ana yinsa ne tsakanin al\’ummomin Jihar Zamfara da ke Arewacin tarayyar Najeriya.

Lamarin dai da ya ki ci ya ki cinyewa tsawon shekaru ana kashe mutane a jihar ya dade da zame wa kowa karfen kafa a yankin da ake kashe kashen da satar kayan jama\’a musamman dabbobi.

A wajen kokarin yin sulhun an ga mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara da kuma manya-manyan jami\’an tsaro.

A ta bakin wani mai aikin Sa kai Usman Danguran Badarawa ya ce ya shiga aikin-sa-kai ne tun lokacin da al\’amari ya yi kamari a tsakaninsu da makiyaya.

Haka shi ma da ake wa lakabi da Buharin Daji cewa ya yi duk lamarin ya samo asali ne da harka ta zama ba daidai ba a tsakanin bangarorin biyu.

Ardo na Shuwarin cewa ya yi lamarin ya lalace ne bayan da aka samu matsaloli a wurare kamar su Dansadau, Dangulbi da Kanoma, Kizara da dai sauran wadansu wurare amma kuma Gwamnati ba ta daukar mataki duk da ana sace masu shanu a tun farkon lamarin.

Fata dai shi ne yaushe za a ga karshen wannan al\’amari tare da fatar samun ci gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here