ANA ZARGIN WANI DAN MAJALISA DA SA A DAURE WANI MATASHI A KANO

    0
    941

    Daga Usman Nasidi

    ANA zargin dan majalisar dattijai mai wakiltar Kano ta arewa Barau Jibrin da sa a kama da kuma tsare wani dan siyasa kuma sojan baka Yakubu Dangawan Jingau a bisa wasu kalamai da ya yi a gidan rediyo na batanci.
    Cikin kalaman da batancin da da ake zargin dan siyasan sun hada da tuhumar asalin karamar hukumar haihuwar Sanatan ta Kabo.
    Sanata Jibrin ya takararsa ta farko zuwa majalisar wakilai a shekarun 1999 zuwa 2003 ya tsaya takarar ne a karamar hukumar Tarauni daga baya kuma a cewar mai zargin, ya koma karamar hukumar Kabo wacce yanzu yake waklilta a majalaisar dattijai.
    Sai dai  bala\’irar Danagawan ta soma ne a lokacin da ya zargi Sanatan a wani shirin siyasa da wani gidan rediyo mai zaman kansa ya ke yi a inda ya ce Sanatan ya yi watsi da \’yan mazabarsa.
    Amma a cewar, wata majiya ta kusa da Sanatan wanda kuma shi ne shugaban kwamitina kulada albaraktun man fetur, ta ce babban abin da ya fusata sanatan shi ne zagin matasahin na cewa, ya kasa biyan kudin kai wani bijimin Sa zuwa garin Minna wurin yayan sanatan. ya kumakara da zai bi sawun ya ga ko mene ne za a yi da bijimin a can. wanda a cewar majiyar, na nufin wani abu kamar tsafi.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here