Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
WANI matashi dan kimanin shekaru 30 ya rataye kansa a kauyen Tsamiya Babba da ke karamar hukumar Gezawa Jihar Kano.
Gawar wannan matashi an tsince ta ne a cikin Gona kuma dukkan alamun da jami\’an tsaro suka bayyana lallai shi ne ya kashe kansa domin an samu matsalar kazantar kashi da sauran alamu a tare da gawar a rataye.
Dalilin da ya sa ake zaton rataye kansa ya yi saboda idanunsa duk sun fito.
Kamar dai yadda jami\’an tsaron suka bayyana cewa an kuma sake gano wata gawar ta mace ita ma da alamun za ta kai shekaru 80 domin dattijuwa ce amma ita ba kazanta kamar gawar matashin.
Sai kuma a Unguwar Badawa ma an samu wata da ta kashe kanta domin wani da za su yi aure ya fasa auren saboda wata larurar da ya gano a tattare da ita sai kawai ta yanke wa kanta hukuncin ta kashe kanta.