AN KARA FARASHIN KUDIN JIRGIN KASA DAGA KADUNA ZUWA ABUJA

0
1007

Daga Usman Nasidi

A ranar Litinin ne, hukumar kula da jiragen kasa (NRC) ta bayar da sanarwar yin karin kudin shiga jirgin kasa daga Kaduna zuwa Babban birnin Tarayya Abuja da kashi 25 wanda kuma tuni ya fara aiki.
A bisa sabon tsarin farashi, daga yanzu fasinjojin da ke amfani da taragar marasa karfi, za su rika biyan Naira 1,050 a maimakon Naira 600 sai kuma masu amfani da taragar Alfarma za su rika biyan Naira 1,500 a maimakon Naira 900.
A wani labarin kuma, Gwamnatin Najeriya ta amince da a karo sababbin taragon jirgen kasa domin jigilan matafiya daga Kaduna zuwa Abuja.
Ministan Sufuri, Hadi Sirika ne ya sanar da hakan wa manema labarai a fadar gwamnati dake Abuja.
Ministan ya ce gwamnati ta yi hakan ne ganin yadda matafiya za su karu musamman daga Kaduna zuwa Abuja nan da wata mai zuwa a dalilin gyaran filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja da za a fara.
Filin jirgin saman Kaduna ne za a yi amfani da shi domin hada-hadan jiragen.sama wanda hakan ya sa za a samu karin yawan mutanen da za su dinga bin hanyardaga Kaduna zuwa Abuja da kuma Abuja zuwa Kaduna.
Kwanakin baya gwamnati ta bada kwangilan gyaran hanyar Kaduna zuwa Abuja duk saboda hakan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here