Za A Taso Keyar \’Yan Najeriya Dubu 37 Daga Jamus

0
1138

Mustapha I Abdullahi, Daga Kaduna

AKALLA \’yan Nijeriya da ke zaune a birane da kauyukan Jamus dubu 37 ne ke zaune a kasar kuma cikin adadin dubu 12 za su gamu da fushin hukuma na a dawo da su gida.

Kamar yadda wasu jami\’an da suke kokarin bunkasa tattalin arziki da duk wata hanyar ci gaban Jamus suka bayyana a Abuja cewa a kalla kashi Casa\’in da Tara cikin dari na masu fakewa a Jamus ba yan gudun hijira ba ne yan Neman aiki ne domin a yanzu ba yaki ake a Nijeriya ba.

Sai dai kamar yadda ministan harkokin wajen Nijeriya ya bayyana cewa ga duk wanda ba shi da dalili a zaman Jamus Gwamnati za ta shirya masa yadda zai dawo gida.

\”Mafi yawan wadansu da ke zaune a Jamus ba \’yan gudun hijira ba ne \’yan neman aikin yi ne kawai\”.

Da irin wannan halin da dimbin yayan Afrika ke tsintar kawunansu musamman a kasashen ketare ya zama wata yar manuniyar da kowa zai yi karatun natsuwa domin inganta nahiyarsa ta Afrika.

Kuma hakika wannan wani kalubale ne da ke  nunin irin matukar bukatar da ake da ita a daukacin nahiyar Afrika na shugabanni da masu basira, hazaka da son rikon gaskiya da amana kowa ya mayar da himma domin kawo ci gaba mai ma\’ana ba a kan takarda ba kawai.

Hakan kuma na nunin lallai sai an canza tunanin yadda a daukacin nahiyar kwazon aiki basira rikon gaskiya da amana tare da mutunta mutane basa aiki a nahiyar Afrika, Wanda hakan ke haifar da ci baya kwarai.

A misali samun takardar shaidar kammala karatun jami\’a shi ya fi komai muhimmanci ko da mutum bai san komai ba a kan abin da yake ikirarin ya karanta.

Kuma mafi yawan jami\’o\’in Nahiyar tuni duniyar karatu ta barsu a can baya amma duk da haka sai masu takardar shaidar kammala karatu ko da kuwa ta karya ce ba komai.

Musamman a Nijeriya za ka ji a kodayaushe Gwamnati na ambatar mutum kaza sun kammala karatun jami\’a ba su da aikin yi ba maganar me wane zai iya yi ba ko masu basira iri kaza da kaza nawa muke da su me kuma za su iya yi?

Duk da a duniya akwai mutane da yawa da ba su da satifiket amma sun kirkiri abubuwan da duniya ke tinkaho kuma mutane ba iyaka suke amfani da su, da alama wannan bai zamar wa Afrika darasi don haka koma baya ke kokarin mamaye ko ina.

Wadanda ke zuwa kasashen Turai ba sa kokarin ganin sun samar da ci gaban da suka gano a can, sai dai ba a san me laifi ba tsakanin su da shugabannin Nahiyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here