Wani Matashi Ya Kashe Mahaifinsa Saboda Aure A Jigawa

0
1053

Rabo Haladu Daga Kaduna

RUNDUNAR \’yan sandan jihar Jigawa ta gurfanar da wani matashi mai kimanin shekaru 25 bisa zarginsa da kashe mahaifinsa ta hanyar amfani da makami.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi cikin dare yayin da mahaifin wanda ake zargin mai kimanin shekaru 65 yake bacci.

Kakakin \’yan sandan jihar Jigawa SP Abdu Jinjiri ya shaida wa manema labarai cewa binciken farko da suka gudanar ya nuna cewa matashin ya kashe mahaifinsa ta hanyar buga masa fartanya da kuma itace bisa tsammanin yayansa ne. Matashin mai suna Abdulhamid Abdullahi ya kullaci yayan nasa ne, bayan ya zarge shi da zuga mahaifinsu kan ya ki amincewa da yunkurin auren da Abdulhamid ke yi.

Su dai Magabatan Abdulhamid na nuna adawa da auren saboda ba shi da sana\’a. Lamarin dai ya fusata matashin, wanda ya yi yunkurin huce haushinsa a kan dan\’uwansa, wanda shi kuma ya garzaya dakin mahaifinsu domin neman mafaka. Rundunar \’yan sandan jihar Jigawa ta ce matashin daga nan ne ya fada wa mahaifin nasa a tsammaninsa yayansa ne a kwancen

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here