Daga Usman Nasidi
RUNDUNAR tsaro ta Civil Defence a ranar Lahadi 21 ga watan Fabrairu shekarar 2017 ta ce, jami\’anta sun samu nasarar ceto wani matashi mai suna Abdulkarim Garba daga hannun wasu da ake zaton masu satar mutane a Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Babban kwamandan rundunar Ibrahim Abdullahi ne ya fadi haka a Maiduguri a wata hira ya ce, masu satar mutanen sun sace matashi Garba ne sun kuma yar da shi a unguwar Njimtilo da misalin karfe 5:00 na yamma a ranar Asabar.
Su kuma jami\’an rundunar suna yawon sintiri a wannan unguwa sai suka cikaro da shi a cikin wani irin yanayi da ya sa suka soma bincikarsa.
Binciken nasu ya nuna cewa, matashin sunansa Abdulkarim Garba dan shekara 15, dan asalin jihar Yobe ne, kuma yana karatu ne makarantar koyon addinin Islama ta El Kanemi.
Shugaban rundunar ya kuma ce, a lokacin da jami\’ansa suka gan shi, ba ya cikin hayyacinsa bai kuma san inda ya ke ba, bai kuma san inda za shi ba.
Sai dai daga baya ne ya yi bayanin cewa, \”abin da zai iya tunawa shi ne ya shiga wata motar haya a mahadar kamfanin Borno Express\”.
\”Amma sai ya tsinci kan shi a Njimtilo cikin mamaki, abin da zai iya tunanawa kawai shi ne a cikin motar ce wani ya barbada masa wata farar hoda wanda hakan ya sa ya rasa hankalinsa\”.
Garba wanda ya auna arziki ya ce, \”da alama wadanda suka sace shi sun fahimci ba za su iya wuce shingen binciken ababben hawa na Njimtilo ba sai suka sauke shi suka kuma gudu\”
ansa suka gan shi, ba ya cikin hayyacinsa bai kuma san inda ya ke ba, bai kuma san inda za shi ba. Sai dai daga baya ne ya yi bayanin cewa,