Jami’an Tsaro Sun Kama Motoci 2 Na Jigilar Shanu A Bayelsa

0
976

MUSA MUHD.KUTAMA, Daga Kalaba

JAMI’AN tsaro a Jihar Bayelsa sun cafke wasu motoci biyu zakure da shanu da aka shigar da su jihar wannan lamari kamar yadda majiyarmu ta samu labari cikin sanarwar da mai magana da yawun Sariake Dickson Gwamnan jihar Daniel Iworiso-Markson ya rattaba wa hannu ya ce motocin biyu za a kai su Imiringi da Ammassoma yankin karamar hukumar Ogbia .

Sanarwar ta kara da cewa ba shanun kadai aka kama ba a’a har masu shanun ma. Da wakilinmu ya tuntubi mai bai wa gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, Dokta Boma Spero-Jack ya tabbatar masa da kamen an yi shi kuma ya kara da cewa masu shanun ma sun ce a yi masu afuwa a sake su domin ba su da masaniyar wannan sabuwar doka ta gwamnatin jihar.

Ya ci gaba da cewa matakin hana kwarorowar Fulani makiyaya zuwa Jihar Bayelsa da ta dauka ba sabon abu ba ne domin a kauce wa fada wa rikici tsakanin makiyayan da manoma don haka ba wai an tsani masu shanun ba ne ko kuma an yi haka da gayya ko wata manufa ta daban ba.

Daga bisani gwamnati ta bayar da umarni a saki shanun kuma a kai su  wani wuri da gwamnati ta kebe domin makiyaya.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here