Fasinja Ya Kashe Dan Acaba Dalilin Naira 50

0
966

MUSA MUHD.KUTAMA, Daga Kalaba

CACAR baki da ta barke tsakanin dan acaba da fasinjansa kan naira 50 ta jawo sanadiyyar ajalin dan acabar, wannan lamari ya faru ne jiya Laraba tsakanin Michael Eze ,wato mai hayar babur din da fasinjansa mai suna Micheal Gabriel. Wannan lamari ya faru ne a yankin karamar hukumar  Igboeze ta arewa da ke Jihar Enugu.

Bayanai da wannan jarida ta samu an ce yarjejeniyar kudin haya wadda tun farko ce aka yi tsakanin dan acavar da fasinjansa kan kudi Naira 50 kacal bayan da ya  kawo fasinjan nasa sai shi mai mashin din wato dan acabar ya nemi ala-tilas sai fasinjan ya kara masa wata Naira 50 kan yadda tun farko suka ji jinga daga nan fe sai sa-in-sa ta barke tsakanin su .wata majiya data bukaci saka ya sunan ta ta yi bayanin ana zargin shi Micheal ne da daukar rodi ya kwada wa Micheal Eze ya fadi somamme daga nan kuma bai kara motsawa ba  sai ya wuce lahira.

Wakilinmu  ya tuntubi kakakin rundunar yan sandan jihar enugu  DSP Amaraizu Ebere, game da lamarin ya kuma tabbatar da afkuwar hakan wanda ake zargi yana hannu yana yi masu bayanai na gamsuwa .

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here