MUSA MUHD.KUTAMA, Daga Kalaba
WATA mata mai suna Foluke Owolewa,wadda ta haihu ta yi ikrari cewa ita ta kashe dan da ta haifa a ranar da ta haihu saboda zargin mijinta ba zai iya ciyar da su ba da kuma iya daukar dawainiyar jegonta ba ya sanya ta yanke shawarar kashe jaririn da ko kwana bai yi ba.
Wannan lamari ya faru ne kauyen Ipamesan ,jihar Ogun, samun labarin aikata hakan ke da wuya sai jama’a suka garzaya suka sanar wa da ‘yan sanda a ofishin su da ke Sango, kuma ba tare da wani jinkiri ba mataimakin shugaban al’ummar kauyen ya jagoranci ‘yan sanda aka kamata .A jawabin da ta yi wa ‘yan sanda a ofishin nasu mai jego Foluke kamar yadda jami’in hulda da jama’a na rundunar Abimbola Oyeyemi ya sanar wa manema labarai ya ce babban jami’in ‘yan sanda mai kula da ofishin Sango Ota SP Akinsola Ogunlewe ne ya jagoranci jami’ansa zuwa unguwar Aninshere inda matar take da zama aka kamata .
Kakakin ‘yan sandan ya kara da cewa daga bayanani da suka ruwaito game da wadda ake zargi an ce ba tun yanzu ba ne take kokarin rika kashe ‘ya’yanta ba idan ta haihu.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ahmed Iliyasu ya bada umarnin a kaita a tsare sashen masu aikata rikakkun laifuka na rundunar.